An yi bikin kaddamar da ayyukan kwashe sojojin Amurka a hukumance da yammacin a filin jirgin sojin sama da ke Birnin Yamai na Jamhiriyyar Nijar.
Tsarin jadawalin da tawwagar jami’an Pentagon ta cimma matsaya a kansa tare da jami’an ma’aikatar tsaron Nijar a ranar 19 ga watan Mayun da ya gabata, shi ne ya kayyade cewa za a ci gaba da ayyukan kwashe dakarun na Amurka har zuwa ranar 15 ga watan Satumba, 2024 a matsayin wa’adin karshe.
- Sojojin Nijar Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Zamfara
- Jamus Za Ta Bar Sansanin Sojinta Na Nijar A Bude Bisa Yarjejeniyar Wucin Gadi
Jami’in Ma’aikatar Pentagon Janar Kenneth Ekman ya yi jawabi a yayin kwarya-kwaryar bikin da aka shirya a filin jirgin sojan saman base 101 da aka fi sani da Escadrille wanda ke matsayin sansanin da kasashe aminnan Nijar suka kwashe kayan ayyukan dakarunsu, inda shi ne aka kaddamar da ayyukan fice-war sojan Amurka daga Nijer.
Tun ranar 16 ga watan Maris, 2024 da hukumomin mulkin sojan Nijar suka ba da sanarwar yanke huldar ayyukan soji da Amurka sakamakon abin da suka ki-ra rashin halaccin yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattabawa hannu a she-karar 2012 da nufin karfafa matakan yaki da ta’addanci.
A ranar 19 ga watan Mayun 2024 ne Amurka da Nijer suka amince da tsarin jadawalin kwashe dakaru 1000 da ‘yan kai da Amurka ta girke a wannan Nijar.
Colonel Major Maman Sani KIAOU shi ne babban kwamandan rundunar sojan kasa, ya ce daga ranar 19 ga watan Mayu dakaru 269 aka kwashe daga ci-kin 946 da ton-ton na kayan aiki da ake shirin ficewa da su daga Nijer saboda haka a wannan karon jirgin sojan Amurka samfarin C 17 GLOBMASTER III zai daga da wani rukuni na wadanan dakaru.
Domin gudanar da ayyukan cikin sauki da fahimta an kafa wani kwamitin had-in gwiwa wanda ya bullo da tsarin da za a tafiyar da lamuran da suka shafi sha’anin ba da izinin sauka da tashin jirage da ratsa sararin samaniya yadda ya kamata, kuma ayarin motocin sojojin Amurka sun tashi daga Ouallam da Diffa zuwa Yamai da Agadez.
Dangane da abubuwan da aka tsayar a yarjejeniyar ta ranar 19 ga watan Mayun 2024 bangarorin sun yi na’am da bukatar inda wasu kwararun sojojin Amurka da za su yi aikin tattara kayayaki a sansanin sojan sama na 101 da ke Yamai da sansani na 201 dake yankin Agadez.
Kafin ranar 15 ga watan Satumban dake tafe ne ya kamata sojojin Amurka su kammala ficewa gaba daya daga Nijar kamar yadda hukumomi suka nuna bukata, matakin da ya sami goyon baya daga mafi yawancin al’ummar kasar.