Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci kungiyoyin kananan masana’antu (NASI) domin kaddamar da kasuwar baje kolin watan Ramadan a dandalin baje koli na filin KACCIMA da ke Zoo Road, cikin kwaryar birnin Kano.
Gwamntin Kano ta ce makasudin wannan kasuwa ta baje koli shi ne, domin sayar da kayyayakin abinci cikin sauki da rangwame saboda saukaka wa al’umm a watan Azumi.
- NCRMIDP Ta Raba Wa ‘Yan Gudun Hijira 700 Kayan Abinci A Katsina
- An Kammala Canja Fasalin Gasar Cin Kofin Zakarun Turai
Gwamnan Kano ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da kasuwar wanda ya sami wakilcin mai ba shi shawara kan harkokin kamfanoni da masana’antu, Hon. Bello Aliyu Kiru, wanda aka gudanar a Jihar Kano.
A jawabin shugaban kungiyar NASI na kasa wanda ya samu wakilcin ma’ajin kungiyar, Dakta Abubakar Tanko Bala ya ce sun gamsu da kokarin NASI a Jihar Kano karkashin shugabancin Aminu Ibrahim Kurawa, wanda shi da mataimakansa suka sami nasarar gayyato shugabanin kasuwannin Kano domin gudanar da wannan biki.
Haka kuma akwai hukumomi irinsu hukumar kula da ingancin kayyakin abinci ta kasa (SON) da shugabanin kungiyoyi irinsu Muazzam Harazimi Aliyu, daga SMEDAN, akwai Rukayya Abdullahi Umar, shugabar kungiyar NWOFBE ta masu sarrafa kayyayakin Abinci zallah ta Arewa, sai kuma Hajiya Gambo Abdullahi, shugabar gamayyar kungiyoyin masu wayar da kan mata (NCWS) da dimbin kungiyoyi duk sun halarci wannan kasuwa ta baje kolin Ramadan.