Karamin ministan cinikayya, masana’antu da raya hadin gwiwa na kasar Uganda David Bahati, ya ce a shekarar nan ta 2024 kadai, an kaddamar da masana’antu 8 masu jarin miliyoyin dalolin Amurka a kasar, wadanda ’yan kasuwar kasar Sin suka zuba jarin kafuwar su, matakin da ya samar da tarin guraben ayyukan yi ga al’ummar Uganda.
Mista Bahati, ya bayyana hakan ne a jiya Litinin, yayin da yake jawabi a cibiyar watsa labarai ta Uganda, don gane da ci gaban da ake samu a fannin raya masana’antun kasar.
- CMG Ya Bayyana Rassan Wuraren Da Za A Yi Liyafar Bikin Bazara
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 14 A Jihar Filato
Ya ce shugaban kasar Yoweri Museveni ne ya jagoranci kaddamar da masana’antu 4 cikin jimillar 8 da aka bude a bana, ciki har da kamfanin Unisteel Investment Uganda Limited, wanda sabon kamfanin sarrafa karafa ne da jarinsa ya kai dalar Amurka miliyan 100, ya kuma samar da guraben aikin yi ga mutane sama da 500.
Baya ga wadannan manyan kamfanoni, wasu kungiyoyi da jam’iyyun gama kai daga sassa masu zaman kan su, sun kafa kamfanoni kanana da mafiya kankanta sama da 250.
Bahati, ya ce sashen masana’antun Uganda ya samar da gudummawar kaso 27.4 bisa dari ga jimillar GDPn kasar, wanda hakan ke da nasaba da fadadar sashen sarrafa hajojin kasar, wanda ya karu da kaso 11 bisa dari cikin rubu’in karshe na shekarar 2023 zuwa 2024.
Daga nan sai ya bayyana sashen sarrafa hajoji a kasar a matsayin bangare mafi girma a fannin raya masana’antun kasar, wanda ke samar da kaso 16.5 bisa dari na GDPn kasar, tare da samar da guraben ayyukan yi na kai tsaye ga sama da mutum miliyan daya. (Saminu Alhassan)