An yi bikin gabatar da shirin bidiyo da babban rukunin gidajen rediyo da talibiji na kasar Sin wato CMG ya shirya, mai taken “Daga Great Wall zuwa MaChu Picchu”, tare da kaddamar da shafin sada zumunta cikin harshen Quechua, a birnin Lima fadar mulkin kasar Peru.
Shugaba kuma babban editan CMG Shen Haixiong, da shugaban lardin Cuzco na kasar Peru Luis Beltrán Pantoja Calvo, da sauran manyan jami’ai sun halarci bikin.
Harshen Quechua na daga cikin harsunan waje 81 da CMG yake amfani da su wajen watsa labarai. Ana amfani da harshen ne a wasu kasashen kudancin nahiyar Amurka ciki har da Peru, da Ecuador, da Bolivia da sauransu. Kazalika, Peru ta shigar da harshen cikin daya daga harsunan gwamnatinta a shekarar 1975. (Amina Xu)