Yayin ziyarar aiki da babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar, Xi Jinping yake yi a kasar Vietnam, yau Litinin, an kaddamar da shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Vietnam a kasar Vietnam.
A wannan rana, an gudanar da bikin hadin gwiwa tsakanin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, da gidan talabijin na Vietnam, game da taron musayar al’adu don murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Sin da Vietnam a birnin Hanoi. Bangarorin biyu za su kara kafa tsarin hadin gwiwa da aka saba, da zurfafa hadin gwiwa a fannonin musayar shirye-shirye, da hadin gwiwa wajen samar da shirye-shirye, da musayar ma’aikata, da mu’amalar fasahohi da dai sauransu, ta yadda za su ba da gudummawa wajen sa kaimi ga sada zumunta tsakanin kasashen biyu. Firaministan Vietnam Phạm Minh Chính ya aike da sako, inda ya taya murnar nasarar gabatar da shirin da kuma kaddamar da bikin.
Bugu da kari, Shen Haixiong, shugaban CMG, ya halarci bikin kuma ya gabatar da jawabi. Ya ce, CMG zai kara yin hadin gwiwa da gidan talabijin na Vietnam, don inganta sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Vietnam. (Safiyah Ma)














