A yau Juma’a, an bude taron koli na Wuzhen, a karkashin laimar taron yanar gizo ko Internet na duniya na shekarar 2025, a garin Wuzhen dake lardin Zhejiang na Sin. Ana sa ran mai da hankali kan batun cika shekaru 10 da gabatar da ra’ayin kafa al’umma mai makomar bai daya a fannin harkoki masu nasaba da yanar gizo, a wajen taron wannan karon, inda za a nuna ci gaban da aka samu a fannin yanar gizo ta duniya, da gudanar da jerin tattaunawa da bukukuwa.
An ce za a gudanar da tarukan dandalin tattaunawa 24, yayin taron kolin Wuzhen na bana, wadanda za su shafi Shawarar Raya Kasa a Duniya, da tattalin arziki na fasahar zamani, da aikin kula da bayanai da alkaluma, da nazarin kimiyya da fasaha bisa amfani da kirkirariyar basira ta AI, da karewa da inganta gadon al’adun gargajiya ta fasahohin zamani, da dai makamantansu.
Ban da haka, tun jiya Alhamis, aka bude bikin baje koli mai taken “Hasken Yanar Gizo”, don nuna sakamakon da aka samu ta fuskar kirkiro fasahohin zamani, da raya masana’antu, da samar da hidimomi, duk ta hanyar amfani da fasahar AI. An ce, wannan biki ya samu halartar kamfanoni da kungiyoyi 670 na kasashe da yankuna 54. (Bello Wang)














