A yau Asabar aka kaddamar da tashar watsa labarai ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ta Sichuan, tare da kaddamar da wasu jerin ayyuka na CMG din a Chengdu babban birnin lardin Sichuan.
Daraktan CMG Shen Haixiong ya halarci taron, inda a ciki jawabinsa ya ce kafar CMG za ta kara lalubo albarkatun dake bangarorin al’adu da yawon bude ido na Sichuan, da gabatar da kyawun al’adun Bashu da karfafa aikin sadarwa cikin ci gaba mai inganci na lardin Sichuan.
Har ila yau, an kaddamar da cibiyar kirkire-kirkiren kimiyya da fasahohin bidiyo na ultra HD da na daukar murya da dakin gwaje gwajen ayyukan watsa labarai na kasa a birnin na Chengdu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp