A ranar 12 ga wata, aka kaddamar da tsarin samar da ruwa mafi girma da kamfanin kasar Sin ya gina a lardin Malanje na kasar Angola, inda shugaban kasar Angola Joao Lourenco ya halarci bikin kaddamarwa.
A gun bikin, shugaba Joao Lourenco ya ce, tsarin zai iya kare yaduwar cututtuka bisa la’akari da yadda yake samar da tsabtaccen ruwa, kuma hakan gudummawa ce ga kyautata rayuwar al’umma.
A nasa bangare, ministan kula da makamashi da ruwa na kasar Joao Baptista Borges ya ce, yadda aka kaddamar da tsarin zai yi matukar inganta karfin samar da ruwa a wurin, lamarin da ya sa shi zama daya daga cikin muhimman ababen more rayuwa na kasar.
Wani jami’in kamfanin da ya dauki nauyin gina tsarin ya bayyana cewa, tsarin na samar da ruwa na kunshe da aikin gina wata masana’antar sarrafa ruwa da kuma wasu ma’adanan ruwa hudu, wanda ya kasance tsarin samar da ruwa na farko da ke aiki a duk tsawon rana a wurin, wanda kuma al’ummar wurin sama da dubu 330 za su amfana da shi.  (Lubabatu)