Mutum-mutumin inji kirar kasar Sin, ya lashe gasar karshe ta tseren mita 100, a gasar wasanni ta mutum-mutumin inji ta duniya ta 2025, da aka yi jiya, a dakin wasan tseren kankara na kasa. Mutum-mutumin inji mai la’akari da yanayi da muhallinsa da ake kira Tian Gong Ultra, wanda cibiyar kera mutum-mutumin inji ta Beijing ta samar ne ya lashe gasar cikin dakika 21.50, wanda ya kaddamar da gasar tseren mita 100 na mutum-mutumi na farko a duniya.
Wannan gasa ta 2025, ita ce irinta na farko da mutum-mutumin inji suka fafata, inda jimilar kungiyoyin wasanni 280 daga kasashe da yankuna 16 suka hadu a Beijing.
Mashirya gasar sun ce manufar ita ce, nunawa da gwajin sabbin nasarorin da aka samu a fasahar kera mutum-mutumin inji ta hanyar gasa, da yayata ci gaban da fasahar ta samu a bangarori daban daban, kamar na gangar jikin mutum-mutumi da kirkirarriyar basira da gano abubuwa da saukaka amfani da aiwatar da abubuwa. (Fa’iza Msutapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp