A yau Alhamis 23 ga wata ne aka gudanar da taron tattaunawa game da raya bangaren al’adu na kasar Sin na shekarar 2024 a birnin Shenzhen na lardin Guangdong.
Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kuma shugaban sashen yada bayanai na kwamitin kolin JKS Li Shulei, ya halarci zaman tare da gabatar da jawabin kaddamarwa.
Taken taron na bana shi ne “Turbar kasar Sin ta zamanantarwa da sabon burin kasar na raya al’adu “, kuma sashen yada bayanai na kwamitin kolin JKS ne ya dauki nauyin shirya shi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp