An kai jirgi samfurin C909, irinsa na farko na ceton rai, zuwa birnin Zhengzhou na lardin Henan dake tsakiyar kasar Sin, ga kamfanin kula da sufurin jiragen sama na Flying Dragon na kasar, inda ya zama irinsa na farko na kasuwanci da aka kera a cikin kasar.
A cewar kamfanin kasar Sin na Commercial Aircraft Corporation da ya kera shi, jirgin ceton samfurin C909, na iya daukar nauyin da ya kai ton 10 da tafiyar kilomita 3,700, kuma zai iya sauka da tashi a filayen jirgin sama dake yankuna masu tudu, kana za a iya fasalta shi ta yadda zai yi jigilar tawagogin lafiya da bayar da taimako a yankuna masu nisa da kuma jigilar marasa lafiya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp