Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta cafke wani mutum da ake zargi da laifin yin sojan gona na aikin ‘yansanda domin karɓar kuɗi daga hannun jama’ar gari da ba su ji ba su gani ba.
Kakakin Rundunar, Abdullahi Kiyawa, ya ce wanda ake zargin, Nasiru Shitu mai shekaru 33 dake zaune a unguwar Ƙofar Waika a Kano, an kama shi ne da yammacin ranar Lahadi a kofar Dawanau a lokacin da yake sanye da kakin ‘yansanda.
Kiyawa ya ce, an kama shi ne da misalin karfe 5 na yamma biyo bayan korafe-korafe da dama na ayyukan karɓar kuɗaɗen jama’a “ba gaira ba dalili” da ɗansandan bogin ke yi a yankin.
A cewar kakakin rundunar ‘yansandan Kano, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, Shitu ba jami’in ‘yansanda ba ne kuma ba konstabulari na musamman ba ne.
Ya kara da cewa, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yayin da ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin sanin girman munanan ayyukansa da kuma duk wani mai hannu a ciki.