Rundunar ‘yansanda a jihar Neja ta kama wasu mutane 30 da ake zargi da hannu wajen aikata sace-sace, kwace da sauran miyagun ayyuka a lokacin Mauludi a garin Minna.
An kama wadanda ake zargin ne a ranar Asabar din da ta gabata, tsakanin karfe 7 na safe zuwa karfe 9 na dare a wurare daban-daban a fadin babban birnin jihar, ciki har da Angwan-Sarki, Limawa, Angwan-Daji, New-Market, Sabon-Gari, Titin Kuta, Obasanjo Complex, Ogbomosho Street, Lagos Street da kuma central roundabout.
- Jarin Da Sin Ta Zuba Kai Tsaye A Kasashe Cikin Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ya Karu Da Kashi 22.9% A 2024
- Gwamna Uba Sani Ya Buƙaci Al’ummar Jihar Kaduna Da Su Yi Rijistar Katin Zaɓe
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Wasiu Abiodun ya fitar a ranar Litinin, ta ce wasu daga cikin wadanda aka kama sun hada da, Abdullahi Ibrahim na Keterengwari, Zahradeen Ibrahim wanda akafi sani da (Legos boy), Dauda Usman, Abubakar Ibrahim, Bashir Safiyanu, Ashiru Rabiu, Abba Abubakar, da kuma Mohammed Abubakar.
Kayayyakin da aka samu daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wukake adduna almakashi, tabar wiwi, shisha, da sauran haramtattun abubuwan maye.
“Ana kan binciken dukkan wadanda ake tuhuma kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bisa laifin aikin dabanci,” in ji Abiodun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp