Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa ta tabbatar da kama wani matashi mai shekaru 26 a duniya mai suna Nura Mas’ud, bisa laifin bankawa kakarsa wuta da ya yi.
Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa, Lawan Adam ne ya tabbatar da faruwar lamarin.
- Ɗan Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ya Rasu
- An Gudanar Da Bikin Murnar Cika Shekaru 10 Da Kafuwar Huldar Abota Bisa Manyan Tsare-Tsare A Duk Fannoni Tsakanin Sin Da Jamus
Lawan ya ce, “A ranar 8 ga watan Oktoba na wannan shekarar, mun samu korafi kan wani abin takaici da ya faru a ƙauyen Ɗan Gwanki da ke ƙaramar Hukumar Sule-Tankarkar a Jihar Jigawa.
“Mun samu labarin wani Nura Mas’ud ya bankawa kakarsa wuta, me shakaru 60 a duniya.
“Yayin da aka garzaya da ita asibiti domin kula da raunukan da ta samu, anan ta rasu”.
To sai dai, rundunar ‘yansandan ta tabbatar da matashin ba shi da cikakkiyar lafiyar ƙwaƙwalwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp