A yau Lahadi ne aka kammala baje kolin kasa da kasa na hada-hadar cinikayyar hidimomi na kasar Sin na shekarar 2025, ko CIFTIS a takaice a nan birnin Beijing. A cewar mashirya bikin, baje kolin ya cimma manyan nasarori sama da 900 a fannonin gine-gine, da fasahar sadarwa, da hada-hadar kudade da sauransu.
CIFTIS na bana, ya gudana ne tsakanin ranakun 10 zuwa 14 ga watan nan na Satumba, bisa jigon “Rungumar fasahohi masu basira, karfafa hada-hadar cinikayyar hidimomi,” ya kuma hallara masu baje hajoji a dandalinsa na zahiri su kusan 2,000, da wasu karin kamfanoni kimanin 5,600 da suka baje nasu hajojin ta yanar gizo. Har ila yau, a cewar mashirya baje kolin, ya zuwa tsakar ranar Lahadin nan, bikin ya karbi baki mahalarta sama da 250,000. (Saminu Alhassan)













