Da yammacin jiya Talata ne aka rufe gasar daliban jami’o’in kasa da kasa ko FISU kaso na 31, a filin taro na kade-kade dake birnin Chengdu, fadar mulkin lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin.
Gasar wadda ta gudana tsakanin ranaikun 28 ga watan Yuli zuwa 8 ga watan Agustan nan. Gasar ta hallara jimillar ’yan wasa 6,500 daga kasashe da yankuna 113, wadanda suka fafata a fannoni 269 na wasanni 18, tare da karya matsayin bajimta sau 22, cikin kwanaki 12 na gudanarta.
’Yar wasan ninkaya ta kasar Sin ajin mata Zhang Yufei, ta kafa tarihin zama mafi samun lambobin yabo a gasar, inda ta kammala da lambobin zinari 9 a dukkanin gasannin da ta fafata.
A bangaren tawagar kasar Sin mai mutane 411, an zabo sama da rabin daliban dake cikinta ne ta hanyar gwajin kwazonsu a mataki na kasa, sun kuma lashe lambobin yabo 178, ciki har da lambobin zinari 103, matakin da ya sanya su kasancewa kan gaba, a fannin lashe lambobin yabo a gasar, baya ga sauran ’yan wasa daga kasashe da yankuna 53, wadanda su ma suka lashe lambobin yabo daban daban, ciki har da 35, wadanda ’yan wasansu suka lashe a kalla lambar zinari daya.
Dan majalissar gudanarwar kasar Sin Shen Yiqin, da mukaddashin shugaban gasar ta FISU Leonz Eder, da babban shugaban kwamitin shirya gasar ta birnin Chengdu Huang Qiang, sun halarci bikin rufe gasar.
A jawabin da ya gabatar, mista Eder ya ayyana rufe gasar, tare da jinjinawa mashiryanta bisa kwazonsu na ganin gasar ta kammala cikin nasara.
Bayan gasar wadda birnin Beijing ya karbi bakunci a shekarar 2001, da wacce birnin Shenzhen ya karbi a bukunci a shekarar 2011, a wannan karo birnin Chengdu, mai tarihin shekaru 2,300 da kafuwa, wanda kuma ke kudu maso yammacin kasar Sin, ya zamo birni na 3 da ya karbi bakuncin gasar ta lokacin zafi, mai gudana duk bayan shekaru biyu-biyu. Kaza lika, wannan ne karon farko da wani birni dake yammacin kasar Sin ya karbi bakuncin babbar gasar wasannin motsa jiki ta kasa da kasa a kasar ta Sin.(Saminu Alhassan)