An gudanar da bikin kammala gasar Olympic ta lokacin zafi ajin matasa, a jiya Jummaa a kauyen wasanni na Diamniadio dake kasar Senegal, gasar da ta kasance irinta ta farko da aka gudanar a wata kasa dake nahiyar Afirka.
An gudanar da bikin rufe gasar ne a killataccen wuri dake kauyen wasannin, inda aka watsa bikin ta kafofin intanet na hukumomin dake da hulda da gasar.
A ranar 31 ga watan Oktoba ne aka bude gasar ta birnin Dakar, wadda ta hallara matasan ’yan wasan motsa jiki kimanin 2,650, wadanda suka fafata neman lashe lambobin yabo, a sassa sama da 150 na wasanni 25 da aka gudanar a Diamniadio, Saly da kuma Dakar. Kasar Sin ce ta lashe lambobin yabo mafiya yawa a gasar, inda ’yan wasanta suka lashe lambobin zinari 18, da na azurfa 8 da na tagulla 7.
Kazalika, a gasar ta bana, wasan nuna fasahar fada na Wushu, ya shiga jerin wasannin da aka fafata lashe lambobin yabo a cikinsa, a karon farko a tarihin gasar ta Olympic. Yan wasan motsa jiki na nahiyar Afirka, sun lashe lambobin yabo 76, ciki har da zinari 27, da azurfa 17 da tagulla 32, adadin da ya dara wanda nahiyar ta lashe a gasar da ta gabaci ta bana, wadda ta gudana a birnin Buenos Aires a shekarar 2018. A wancan lokacin ’yan wasan Afirka, sun lashe lambobin yabo 56 ne.
Har ila yau, a gasar ta bana, tawagogin Afirka biyar sun kasance cikin tawagogi 10 dake sahun gaba a lashe lambobin yabo na gasar.Da take tsokaci yayin taron manema labarai na bikin rufe gasar a ranar Alhamis, shugabar hukumar shirya gasar Olympic ta kasa da kasa ko IOC Kirsty Coventry, ta ce sakamakon da aka samu, ya shaida bunkasar zuba jari da ake samu a fannin wasanni a sassan nahiyar Afirka.
A nasa jawabin kuwa, babban jamiin tsare-tsare a kwamitin shirya gasar ta Olympic ta Dakar ta 2026 Ibrahima Wade, cewa ya yi Senegal ta sake fito da kanta a dandamalin kasa da kasa da rubi 2.7, yayin da gasar ta cika kwanaki 9 da budewa.
Wade, ya kara da cewa, gasar Olympic ta matasa, da wasanni da ruhin Olympic, muhimman ginshikai ne na daga matsayin Senegal da inganta kimar kasar. Kuma hakan shi ne mizanin awon nasarar gasannin da aka gudanar. (Saminu Alhassan)













