An kammala babbar gasar tseren dawaki ta ƙasa da ƙasa da aka gabatar a Kano ranar Lahadi da ƙungiyar TURF CLUB ta shirya a jihar Kano.
Daruruwan mutane ne suka halarci gasar ta kwanaki biyu da aka shirya ta tseren dawakai mai mita 1600.
Jihohin da suka shiga gasar sun haɗa da Jihohin Kano da Sakkwaoo da Neja da Bauchi da Kebbi da kuma waɗansu masu tseren doki daga Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso.
Mohammed Jabo daga jihar Sakkkwato ne ya lashe Kofin Zazzau tare da samun kyautar N300,000.
Gobara Ta Ƙone Ofishin ‘Yan Sanda A Kano
Hukumar Karɓar Ƙorafi Da Yaƙi Da Rashawa Ta Kwace Rumbuna 10 Da Aka Ɓoye Abinci A Kano
Ibrahim Bandi daga jihar Kebbi, inda shi kuma ya lashe Kofin Nupe, sai kuma Zabqa da ya lashe Kofin ‘Arewa Nigeria Republic’ tare da kyautar kudi N300,000.
Lamiɗo kuma daga Jamhuriyar Nijar shi ya lashe gasar Kofin Gwamna Abba Kabir Yusuf, sai Kofin Kwankwaso da wani daga ƙasar Burkina Faso ya lashe.
Bayan kammala raba kyautukan, wakilin Gwamnan Kano a wurin, shugaban ma’aikatan fadar fadar gwamnatin Kano, Alhaji Shehu Sagagi, ya ce gwamnati za ta yi kokarin ganin ta inganta gasar tseren dawaki ta yadda za ta zama tamkar sauran gasannin dawakai da ake yi a duniya.
Sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci taron ciki har da shugaban kungiyar ‘Turf club’ na Kano, Alhaji Ibrahim, ya yaba da irin gudunmawar da gwamnatin Kano da Bankin First Bank suka bayar da a yayin gudanar da wannan gasar.