An kammala gasa karo na 9, ta wasannin lokacin hunturu ta kasashen Asiya a jiya Juma’a a birnin Harbin, bayan gasar wadda ta shafe kwanaki ana yinta, ta samu manyan nasarori a tarihin tawagogi da dama.
Firaministan Sin Li Qiang, ya halarci bikin rufe gasar mai taken abota, a cibiyar taro da nune-nune da wasanni ta kasa da kasa dake birnin Harbin, inda mataimaki na 1 na shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta nahiyar Asiya (OCA), Timothy Fok Tsun-tsing ya rufe gasar a hukumance.
- Isra’ila Ta Fara Sakin Fursunonin Falasɗinawa 369, Ciki Har Da Waɗanda Aka Yanke Wa Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai
- Sulalewar Likitoci Zuwa kasashen Waje: ‘Likita Guda Na Duba Masu Cutar Kansa 1,800
Yayin da wannan ne karo na farko da kasashen Cambodia da Saudiyya suka halarci gasar ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya, gasar ta bana ta kafa tarihi inda ta yi maraba da ‘yan wasa sama da 1,200 daga kasashe da yankuna 34, lamarin da ya sa ta zama mafi girma a tarihi a fannin mahalarta.
Gasar wadda aka bude a ranar 7 ga watan Fabreiru, ta kunshi shirye-hirye 64 a fannoni 11 da wasanni 6. Kasar Sin ta samu lambobin zinare 32 da azurfa 27 da tagulla 26, inda ta zo ta daya a teburin lambobin yabo, wanda ya yi daidai da yawan lambobin zinare da Kazakhstan ta lashe a gasar karo na 7 da aka yi a Astana da Almaty a 2011.
An sauke tutar kwamitin OCA, kana an kunna taken kwamitin, inda magajin garin Harbin Wang Hesheng ya mika tutar ga Timothy Fok, yayin da shi kuma ya mika ta ga ministan wasanni na kasar Saudiyya, yarima Abdulaziz bin Turki Al-Faisal. A karo na farko, kasar Saudiyya za ta karbi bakuncin gasar ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya a shekarar 2029. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)