Ƙungiyar Masu dauke da Cutar Kansa a Nijeriya (NCS) ta ce, yawan ficewar ma’aikatan kiwon lafiya zuwa kasashen waje na matukar shafar kula da lafiyar masu fama da cutar Kansa a Nijeriya.
Shugaban kungiyar masu dauke da cutar Kansa, Farfesa Abidemi Emmanuel Omonisi, shi ne ya shaida hakan a hirarsa da ‘yan jarida yayin bikin tunawa da ranar masu dauke da cutar Kansa ta duniya.
Farfesa Omonisi ya ce karancin yanayin aiki da rashin kayan aiki, matsalar tsaro, karancin rayuwa mai inganci da
- Yajin Aikin Likitoci Ya Tsayar Da Al’amura A Asibitocin Abuja
- Ƙungiyar Likitoci Ta Buƙaci Dakatar Da Kwamishina Kan Zargin Cin Zarafin Likita A Kano
karancin kudi a sashin kiwon lafiya na daga cikin dalilan da suke sanya likitocin da ke jinyar Kansa ficewa daga Nijeriya zuwa kasashen waje.
Don haka ne ya roki Shugaban kasa Bola Tinubu da ya yi duk mai yiyuwa wajen magance matsalolin da suke janyo sulalewar likitoci daga Nijeriya zuwa kasashen waje domin kyautata kiwon lafiya a kasar nan.
Ya ce kungiyar ta lura da yadda ake samun karuwar wasu cututtukan daji da aka yi watsi da su a Nijeriya kamar cutar Kansar colo-rectal, yara, obarian, da kuma ciwon daji na jini.
Ya yi kira ga ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya, da ta mai da hankali sosai kan cutar daji da aka yi watsi da su a Nijeriya.
Shugaban NCS ya kuma bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta ware naira biliyan 25 don sauya tsarin kiwon lafiyar cutar Kansa zuwa asusun inshorar lafiya. Ya kara da cewa, NCS ta bukaci majalisar dokoki ta kasa da gwamnatin tarayya da su dace da karin kudade don rufe ba da tallafin naira biliyan 97.2 a cikin shirin nan na yaki da cutar Kanjamau na kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp