Rukunin masana’antun makamashin nukiliya na kasar Sin CNNC ya ce, an kammala hada tushen sashe na karamin injin sarrafa makamashin nukiliya wato small modular reactor (SMR) na farko a duniya da aka yi wa lakabi da Linglong One.
Wannan shi ne kololuwar aikin hada Linglong One, wanda ke wakiltar wani mataki a tarihi na takaita makamashin nukiliyar duniya da kuma tabbatar da cewa kasar Sin ce kan gaba a duniya wajen gina SMR na zamani. (Mai fassara: Yahaya)