“Dukkanninmu mun yi matukar damuwa a game da yiwuwar hadarin fadawa cikin yaki gadan-gadan a yankin saboda abin da ke faruwa a DRC
Masu nazarin al’amuran yanki-yanki, na kira da a gaggauta aiwatar da shawarwarin da aka cimma a wurin taron kungiyar Tarayyar Afirka (AU) na baya-bayan da aka yi a kasar Habasha. Batutuwan da aka fi raja’a kansu a taron su ne tattaunawa akan tashe-tashen hankula a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC), da Sudan, da kuma tasirin da janye tallafin da Amurka ta yi, zai yi nahiyar.
- Kayan Abinci: Gwamnatin Nijeriya Ta Buƙaci ‘Yan Kasuwa Su Rage Farashi
- Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Kara Haraji
Wakilin Muryar Amurka a Abuja Timothy Obiezu ya ruwaito cewa, shugabannin Afurka da wakilai daga kasashe sama da 50 sun hallara a Addis Ababa don gudanar da babban taron Tarayyar Afirka karo na 38 da zai gudana tsakanin ranar Asabar da Lahadi.
Timothy, ya ruwaito cewa, Kwamishinan Harkokin Siyasa, Zaman Lafiya, da al’amuran tsaro na kungiyar ta AU, Bankole Adeoye, ya ce: “Dukkanninmu mun yi matukar damuwa a game da yiwuwar hadarin fadawa cikin yaki gadan- gadan a yankin saboda abin da ke faruwa a DRC. Mun yi ta nanata bukatar a kai zuciya nesa, tare da kiran ‘yan tawayen M23 da magoya bayansu da su kwance damara su kuma janye.”
Sai dai, Senata Iroegbu, mai nazarin al’amuran tsaro, ya ce akwai bukatar shugabannin na Afirka su yi aikata duk abin da suke furtawa da baka wannan karon:
“Idan ba a dau matakin da ya dace akan abin da ke faruwa a DRC ba, al’amarin zai faskara. Ba batun fitar da takardar jawabin bayan taro ne kawai muke yi ba. Dole a biyo bayan hakan da wasu muhimman matakai ko tsare tsare da zasu tabbatar da cewa an gabatar da wadannan al’amura kan teburin shawara tare da nemo mafita irin wanda ya dace da Afurka don warware matsalolin Afurka.”