Kwamitin tsakiya na 20 na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ya gudanar da cikakken zamansa na hudu a birnin Beijing daga ranar Litinin zuwa Alhamis.
Mahalarta taron sun tattauna tare da amincewa da shawarwarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar na tsara shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma na shekaru biyar-biyar karo na 15, kamar yadda sanarwar bayan taron ta bayyana a yau Alhamis.
Babban sakataren kwamitin kolin JKS, Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, a halin yanzu, kasar Sin tana gab da cimma manyan manufofi da ayyukan da aka tsara a shirin shekaru biyar-biyar karo na 14.
A cewar sanarwar, shirin na shekaru biyar-biyar na 15 da za a yi aiki da shi daga shekarar 2026 zuwa ta 2030, zai kasance muhimmi yayin da kasar ke kokarin karfafa ginshikai da kuma samun ci gaba a dukkan fannoni don cimma burin zamanantarwa a turbar gurguzu nan da shekarar 2035, kuma hakan zai zama wata babbar hanyar da za ta sada zamanin baya da na nan gaba.
A wurin taron, kwamitin tsakiya na JKS ya kafa wasu tsare-tsare da za su zama jagora kan bunkasa harkokin tattalin arziki da walwalar al’umma a cikin shirin na shekaru biyar-biyar na 15 wadanda suka hada da sake tabbatar da shugabancin jam’iyyar baki daya, da sanya kula da mutane a gaba da komai, da neman samun ingantaccen ci gaba, da cikakkiyar zurfafa gyare-gyare a gida, da karfafa cudanya tsakanin kasuwa mai albarka da gwamnati mai kwazon aiki, da kuma tabbatar da samun ci gaba da inganta tsaro.
Har ila yau, kwamitin tsakiya na JKS ya shata wasu manyan manufofi game da shirin shekaru biyar-biyar na 15 da suka hada da gagarumar zurfafawa wajen samun ci gaba mai inganci, da ingantacciyar habaka dogaro da kai da karfin ci gaban kimiyya da fasaha, da cimma sabbin nasarori a cikin kara zurfafa gyare-gyare a gida gaba daya, da samun ci gaban al’adu da dabi’a a cikin al’umma a zahirance, da kara inganta jin dadin rayuwa, da samun manyan sabbin ci gaba wajen zurfafa Shirin samar da kyakkyawar kasar Sin, da kuma kara samun ci gaba wajen karfafa garkuwar tsaron kasa.
A gobe Jumma’a ne kwamitin tsakiya na JKS zai gudanar da taron manema labarai kan ka’idoji da kudurorin da aka cimma a cikakken zaman taro na hudu na kwamitin kolin JKS na 20. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














