A yau Jumma’a 21 ga watan Nuwamba ne aka gudanar da taron tattaunawa kan yadda aka tsara shawarwarin da ‘yan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin suka bayar.
An bayyana cewa, a zaman taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 a watan Maris na wannan shekara, wakilai sun gabatar da shawarwari 9,160 kan fannoni daban daban bisa ka’idojin da doka ta shimfida.
Bayan nazari da tantance kowace shawara daya-bayan-daya, an mika su ga rukunoni masu alaka 211 domin su yi bincike da kuma tsara yadda za a tafiyar da su. An kuma kammala dukkansu a bisa jadawalin da aka tsara tare da mayar da amsa ga wakilan jama’ar. (Abdulrazaq Yahuza Jere)














