A jiya Asabar ne aka kawo karshen zangon farko na baje kolin Canton Fair karo na 136, inda manema labarai na kafar CMG suka ce cibiyar lura da shige da fice ta gundumar Baiyun na birnin Guangzhou inda baje kolin ke gudana, ta tabbatar da cewa tun bude baje kolin na wannan karo a ranar 15 ga watan Oktoban nan, adadin mutane dake shiga da masu fita ta filin jiragen sama na Baiyun ya haura 210,000, adadin da ya karu da kaso 16 bisa dari, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na baje kolin lokacin baraza da ya gabata.
Cikin wannan adadi, sama da baki ‘yan kasashen waje 60,000 ne suka shiga ta tashar, matakin da ya nuna karin karbuwar baje kolin na Canton Fair tsakanin ‘yan kasuwar kasa da kasa. A lokaci guda kuma, tsare tsaren baiwa jama’a damar shige da fice cikin kasar Sin, da suka hada da fadada yawan kasashen da Sin ke baiwa al’ummun su damar shigowa ba tare da bukatar visa ba, sun haifar da fadadar adadin mutane dake shiga birnin. Yanzu haka dai jami’an lura da shige da fice ta tashar gundumar Baiyun dake birnin Guangzhou, sun yi has ashen adadin masu shiga birnin, yayin baje kolin na Canton Fair, zai kai kimamin mutane 45,000 a kowace rana.
Domin ci gaba, da jure ba da hidima ga fasinjoji dake tururuwa ta tashar, an tsara samar da hanya ta musamman domin hidimar masu halartar “Canton Fair”, inda aka baza ‘yan sanda masu jin harsuna daban daban, don baiwa masu shiga birnin hidimomin da suke bukata, tare da kara kyautata tsare tsaren shige da ficen jiragen dakon kaya da jami’ai, da samar da karin matakan saukaka harkoki yadda ya kamata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)