Sabbin alkaluman da babbar hukumar kula da haraji ta kasar Sin ta bayar yau 17 ga wata sun nuna cewa, a cikin watannin tara na farkon bana, kamfanoni sun kara zuba jari wajen kirkire-kirkire, kuma sabbin masana’antu bisa manyan tsare-tsare sun ci gaba da habaka. Lamarin da ya shaida cewa, ana samun ci gaba cikin sauri wajen raya sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi mai dorewa ta kasar Sin.
Zhang Bin, darektan kwamitin jam’iyyar kwaminis ta Sin dake cibiyar nazarin dabarun tattalin arziki da hada hadar kudi ta kwalejin kimiyyar zamantakewar al’umma ta kasar Sin,ya bayyana cewa, bisa alkaluman da hukumar harajin ta fitar, ana iya ganin cewa, ana kara habaka sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi mai dorewa a kasar Sin, lamarin da zai taimaka sosai wajen bunkasuwar ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.(Amina Xu)