Wasu gungun masunta da manoma dauke da baka da kibau sun samu nasarar kashe dorinar ruwa da ta kashe Maigadin sarkin Lambun Sarkin Yauri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi tare da raunata wani masunci a kogin Gungun Sarki da ke garin Yauri a jihar Kebbi. Inda a halin yanzu masuncin ke jinya a asibitin koyarwa ta Usmanu Dan fodiyo da ke jihar Sakkwato don kula da lafiyarsa.
Gwamnan Jihar, Nasir Idris ne ya bada umurnin ga al’ummar yankin da su fantsama fagen farautar dorinar su kashe ta, sakon hakan ya fito ne ta hannun mai martaba Sarkin Yauri, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi.
- Sanata Sani Ya Nemi Tinubu Ya Saki Masu Zanga-zanga Da Ke Tsare
- Jihar Kogi Ta Amince Da Naira 72,000 Mafi Karancin Albashin Ma’aikata
A yayin da wakilinmu ya samu zantawa da Alhaji Nasiru Sarki, Mayanan Gungun wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho, inda ya bayyana cewa masunta da manoman sun fantsama cikin kogin Gungun Sarki ne a safiyar ranar Litinin.
A cewar Mayanan Gungun, ‘yan kungiyar sun fara kashe diyar dorinar ne da karfe 11 na safe, sannan suka kashe uwar dorinar da karfe 3 na rana. Daga nan ne suka kai gawar dorinar zuwa fadar Hakimin Gungu, Alhaji Kasimu Aliyu, inda aka fede namanta aka Kuma rarraba naman nata ga jama’ar Yankin har ma da wasu daga garin Yauri, Inji Mayanan Gungun Alhaji Nasir Sarki.
Hakazalika ya ce, “Al’ummar Masarautar Yauri dai sun ji dadi kan nasarar da aka samu kan kashe dorinar ita da diyarta saboda ta dauko hanyar hallaka jama’armu wannan al’amari ya yi ma duk dan yankin masarautar Yauri dadi. Haka kuma sun bayyana godiyarsu ga Gwamna Nasir Idris da Sarkin, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi bisa wannan mataki da suka dauka na bada umurni na hallaka wannan dorinar ita da diyarta”.
Bugu da kari, Mayanan Gungun ya kara da cewa, “Wannan lamarin dai bai zo da mamaki ba, domin a mokonin baya an sha samun rahotannin hare-haren wannan dorinar har ta Kashe Mai-Gadin Lambun Sarkin Yauri, a cikin watan Satumbar 2024, wanda ke kamun kifi mai shekaru 60, mai suna Malam Usman Maigadi.