An tabbatar da kashe wasu Kasurguman jagororin ‘yan bindiga biyu, Sani Black da Kachalla Makore a Zamfara.
‘Yan ta’addan biyu na da alhakin kai hare-haren ta’addanci a gundumomin Dansadau da kewaye da kuma wasu sassan karamar hukumar Maru.
- Gwamnan Anambra Ya Amince Da Biyan Mafi Karancin Albashi Na Naira 70,000
- Adadin Tashoshin Sadarwa Na 5G Ya Kai Miliyan 4 A Kasar Sin
Da yake tabbatar da kisan, babban mai bai wa gwamnan jihar Zamfara shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa, Alhaji Mustapha Jafaru Kaura, ya ce, an kashe Sani Black ne a ranar Lahadin da ta gabata a kauyen Yar-Tasha yayin da kuma aka kashe Kachalla Makore a ranar Talata a kauyen Kunkeli da ke karamar hukumar Maru a jihar.
Kaura ya bayyana cewa, an kashe fitattun jagororin ‘yan bindigan biyu ne tare da wasu abokan ta’addancinsu su 23 a wani farmakin hadin gwiwa da jami’an hukumar kare hakkin jama’a ta jihar Zamfara (CPG) da sojojin Nijeriya suka kai.
“Bayan an kashe Sani Black a wani harin kwantan bauna da aka yi a kauyen Yar’Tasha a ranar Lahadi, 22 ga Satumba, 2024, Kachalla Makore ya tattaro mutanensa a ranar Talata, 24 ga watan Satumba ya nufi Yar-Tasha domin kwato gawar Black da kuma daukar fansa.
“An yi nasara shi ma an yi masa kwanton bauna kuma aka kashe shi a kauyen Kunkeli da ke gundumar Dansadau a karamar hukumar Maru.
“An kashe Sani Black ne tare da mutanensa guda takwas yayin da aka kashe Makore tare da mutanensa 15.
“Makore ya kona motar sulke ta sojoji tare da raunata wasu sojoji biyu a lokacin arangamar da jami’an tsaron a kauyen Kunkeli,” inji shi.