Wasu ’yan bindiga sun kashe wani fitaccen manomi a Kauyen Akor dake unguwar Nzorob a Karamar Hukumar Guma a Jihar Binuwai, Terzungwe Shaku bayan an karbi kudin fansa na Naira miliyan 5.5 daga iyalansa.
Jaridar PUNCH Metro ta gano cewa an yi garkuwa da mamacin ne kafin bikin sabuwar shekara kuma masu garkuwa da mutanen sun nemi Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa.
- Yadda Kuncin Rayuwa Da Matsalar Tattalin Arziki Ke Kara Haifar Da Rikice-rikice Tsakanin ‘Yan Haya Da Masu Gidaje
- Kauyuka Suna Kokarin Neman Cimma Burin Samun Wadata Tare A Kasar Sin
Wata majiyar dangi da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, “Gaskiya ne, Akor kauyena ne. Shi (Terzungwe) yana da kantin sayar da kayayyaki a Akor, a farkon shekarar bara ne Fulani makiyaya suka far masa.
“Amma a wannan karon, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi, dab da shiga sabuwar shekara, suka tafi da shi kusan mako biyu. Sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 10 amma iyalansa sun yi shawarwari da su inda suka kai kudin fansa Naira miliyan 5.5.
“Abin takaici, ‘yan bindigar sun kashe shi ne a daidai inda suka umurci ‘yan uwa su ajiye kudin fansa. Abin da ya faru shi ne, an karshe wadanda suka sace shi ne suka harbe shi suka kashe shi.”
A halin da ake ciki, da aka tuntubi Shugaban Karamar Hukumar Guma da kuma rundunar ‘yansandan jihar sun ce ba su da labarin faruwar lamarin.
Shugaban Karamar Hukumar Guma, Maurice Orwough, ya ce, “Ban san da faruwar lamarin ba.”