Akalla masunta 31 ne aka kashe yayin da wasu 40 suka yi batan dabo yayin da wasu ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suka kai wani mummunan hari a Tunbun Rogo – wani kauye da ake kamun kifi a karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno, a daren ranar Talata.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba ga LEADERSHIP a Maiduguri, Shugaban Kungiyar Dillalan Kifi ta Nijeriya, Mohammed Laminu, ya ce wannan mummunan labari ya tayar wa ‘ya’yan kungiyar da hankali.
- Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Dawo Da Tsohon Taken Nijeriya
- ‘Yansanda Sun Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Kwato Kudin Fansa A Kaduna
A cewar wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa, ‘yan ta’addar sun kashe masunta 31, inda iyalai da dama ke jiran labarin ‘yan uwansu.
“Gawarwakin wadanda iftila’in ya rutsa da su, na jibge a cikin daji, yayin da sauran da suka gudu zuwa dazuzzuka suka fara dawowa da raunuka, suna karbar magani daga sansanin sojoji dake Cross Kauwa.
“’Yan ta’addan sun far wa yankin ne dauke da makamai, inda suka zagaye masuntan sannan suka bude wuta, harin ya faru ne bayan da sojoji suka umurci masuntan da su fice daga yankin, amma duk da bin umarnin da aka ba su, ‘yan ta’addan sai da suka far musu.”
Majiyar ta ci gaba da cewa,”‘yan ta’addan ne suka tara mu, inda suka ce suna son yi mana wa’azi ne, sai kwamandansu ya bayar da umarnin a kashe mu, nan take suka kashe masunta 31, kuma sama da 40 daga cikinmu muka yi nasarar tserewa.
“Kwamandan ya umarci a hukunta daya daga cikin ‘yan ta’addan saboda ya bar wasu daga cikinmu sun gudu.”
Wadanda iftila’in ya afka mawa masunta ne daga garuruwan Monguno, Doron Baga, Cross Kauwa, da Baga.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da hukumomin sojin Nijeriya ko wata hukumar tsaro suka fitar kan harin ba har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoto.