Akalla mutane uku da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka mutu wadanda suka mamaye sakatariyar gwamnatin jihar Oyo da ke Ibadan.
Kazalika wasu biyar daga cikinsu sun shiga hannun jami’an tsaro, a ranar Asabar.
- Abincin Da Ke Kara Wadatar Ruwan Maniyyi
- Shugaban Bankin Duniya: Matakan Kasar Sin Na Tinkarar Sauyin Yanayi Abin Burgewa Ne
Maharan sun gamu da ajalinsu ne yayin da suka yi arangama da jami’an tsaro a sakatariyar jihar yayin da suke kokarin kwace iko da ofishin gwamnatin jihar.
Maharan da suka mamaye sakatariyar na sanye da kakin sojoji dauke da tutar da ke suke kokarin kafa kasar Yarbawa da ita.
Maharan sun afkawa sakatariyar jihar dauke da muggan makamai da nufin kwace iko da ofishin gwamna da na ‘yan majalisun wakilan jihar.
A halin da ake ciki, mai rajin kafa kasar Yarbawa, Cif Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya nesanta kansa da harin.
Igboho wanda yayin kaurin suna wajen rajin kafa kasar Yarabawa, ya ce ya kamata a gudanar da bincike don gano mutanen da suka kai harin.
Ya zuwa yanzu dai an baza jami’an tsaro a birnin domin tabbatar da doka da oda.