Sanata David Jimkuta, mai wakiltar Taraba ta Kudu a Majalisar Dokoki, kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kawar da talauci, ya bayyana cewa rahoton tsaro ya tabbatar da kisan mutane 700 a mazabarsa a Karamar Hukumar Usa da Takum a Jihar Taraba cikin watanni uku.
Ya kara da cewa ‘yan bindiga sun lalata kauyuka sama da 50 a karamar hukumar.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sama Da 100 a Kauyen Filato
- Sojojin Faransa Sun Kammala Ficewa Daga Nijar Gaba Daya
Sanata Jimkuta ya yi wadannan kalamai ne yayin da yake jawabi ga ‘yan jarida a Wukari, hedikwatar Karamar Hukumar Wukari a ranar Talata.
Ya nuna damuwa game da yadda ‘yan bindiga suka lalata USSA da Takum, inda duk manoma suka tsere don tsira da rayuwarsu.
Ya yi gargadin, nan ba da jimawa ba wannan lamari zai iya haifar da karancin abinci a jihar.
Jimkuta ya bukaci hukumomin tsaro da ke aiki a jihar da su kara kaimi da kuma dakile matsalar rashin abinci ta hanyar kawar da ‘yan bindiga daga maboyarsu da bai wa manoma damar ci gaba da ayyukansu.
“Me zai hana a hada kai da mazauna yankin don samun ingantattun bayanai da kuma kai hari ga maboyar ‘yan bindigar?,” in ji Jimkuta.
Sanatan ya kuma yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya ayyana dokar ta baci kan tsaro a yankunan Takum-Usa don bai wa manoma damar komawa gonakinsu.