Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutane da dama a ranar Lahadin da ta gabata a wasu hare-hare daban-daban da aka kai kan al’umomin Effeche da Igama a gundumar Edumoga Ehaje da ke karamar hukumar Okpokwu ta jihar Benuwai.
A ranar Lahadin da ta gabata, an ce akalla mutane 11 ne suka mutu a wani hari da aka kai da sanyin safiyar ranar Lahadi a Igama.
Harin da aka kai garin Effeche, a cewar wasu mazauna kauyen da suka zanta da wakilin Jaridar Daily trust ta wayar tarho, a lokacin yace yanzu haka, maharan suna cikin garin suna farmakin Jama’a a dai-dai misalin karfe 9:30 na dare.
Mazauna yankin sun ce maharan sun yiwa al’ummar Igama kawanya ne da misalin karfe 4 na safiyar Lahadi inda suka bude wuta kan mutanen kauyen.
Rahotanni sun ce sun kona kusan dukkan gine-ginen da ke yankin.
Mazauna kauyen sun ce an gano akalla gawarwaki 11 yayin da ake kan binciken sauran wadanda lamarin ya rutsa da su.
Sai dai shugabar karamar hukumar Okpokwu, Amina Audu, ta shaida wa manema labarai cewa ta karbi gawarwaki uku a Okpoga, hedikwatar karamar hukumar, yayin da aka kawo gawarwaki shida daga garin Igama, daya daga cikin kauyukan da lamarin ya shafa.
Amina ta bayyana cewa maharan sun kai farmaki a cikin al’ummar ne tsakanin karfe 4 na safe zuwa 6 na safe, inda ta kara da cewa sun kona duk gidajen jama’ar.