Zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar ayau Asabar a jihar Benuwe ya gamu da tashe-tashen hankula a wasu sassan jihar.
Akalla mutane shida ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata yayin zaben.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, jami’an tsaro sun harbe wasu mutane shida a karamar hukumar Gboko da ke jihar bisa zarginsu da yunkurin sace akwatunan zabe.
An tattaro cewa mutane shidan da jami’an tsaro suka kashe a wurare daban-daban, suna kokarin cika burin masu gidansu ‘yan siyasa ne masu burin lashe zabe ta ko wane hali.