Aƙalla makiyaya 10 aka kashe a wani harin ramuwar gayya da aka kai bisa kuskure a wani gidan Fulani da ke kauyen Tilli, ƙaramar hukumar Bunza a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne bayan an kashe wani ɗan sa-kai a yankin, inda aka ɗora laifin a kan Fulani mazauna garin, wanda kuma lamarin ba haka yake ba.
- APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba
- Wakilan Sin Da Na Amurka Sun Yi Tattaunawa Mai Ma’ana Da Zurfi Da Kuma Amfani
“Waɗanda suka kai harin sun yi tunanin Fulani ne suka kashe ɗan sa-kai, don haka suka kai musu farmaki a gidajensu, suka kashe mutane sama da 10,” in ji wani mazaunin yankin.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, ya ziyarci yankin domin jajanta wa iyalan waɗanda abin ya shafa.
Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya ce har yanzu ba su samu cikakken rahoton faruwar lamarin ba, amma suna bincike kuma za su fitar da bayani nan gaba.














