Wani rikici mai muni da ya ɓarke tsakanin makiyaya Fulani da manoma Gwari a ƙauyen Kpowi, da ke yankin Fuka na Ƙaramar Hukumar Munya a Jihar Neja, ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama.
Rikicin ya faru ne a ranar 2 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, bayan wata taƙaddama da ta taso kan zargin shiga gonaki da kuma lalata amfanin gona.
- Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus
- Darajar Hajojin Da Aka Fitar Waje Daga Birnin Shanghai Ta Kai Yuan Biliyan 629 Cikin Watanni Hudu Na Farkon Shekarar Bana
Lamarin ya fara da gardama sannan ya rikiɗe zuwa faɗa tsakanin ɓangarorin biyu.
Rahotanni daga yankin sun ce mutum shida daga ɓangaren Fulani da mutum huɗu daga ɓangaren Gwari sun samu raunuka.
Dukkaninsu an garzaya da su Asibitin Gwamnati na Kaffin-Koro domin kula da su, amma wani daga cikin waɗanda suka jikkata mai suna Ahmadu Bature ya rasu.
Jami’an tsaro sun isa yankin domin hana rikicin ci gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya.














