Wani Rahoto, ya nuna cewa akalla jami’an ‘yansanda 229 aka kashe a lokacin da suke bakin aiki, daga tsakanin watan Janairun shekarar 2023 zuwa Oktoban 2024.
Rahoton wanda jaridar Daily Trust ta wallafa, ya nuna cewa jami’an ‘yansanda sun gamu da ajalinsu ne a hannun ‘yan bindiga da mayakan Boko Haram da sauran masu aikata laifuka.
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Fahimtar Kasar SinÂ
- Rabiu Ali Ya Samu Gayyata Domin Wakiltar Nijeriya A Wasannin CHAN
Rahoton ya ce a 2023 kadai, jami’an ‘yansanda 118 aka kashe, sannan an sake kashe wasu 111 a watannin 10 na farkon wannan shekarar.
Na baya-bayan dai shi ne kisan ASP Augustine Osupayi da ke aiki da rundunar ‘yansanda a Jihar Legas, wanda aka kashe a watan Oktoban da ya gabata.
An kashe shi a lokacin da shi da tawagarsa suka yi kokarin dakatar da wasu daga daukar doka a hannunsu a yankin Agage.
Wasu ‘yansanda da aka tattauna da su kan lamarin, sun ce hakan ba zai sa su yi kasa a gwiwa wajen gudanar da aikinsu ba.
To sai dai rundunar ‘yansandan Nijeriya ba ta ce komai ba kan wannan rahoto ba, duk da cewar Sufeto-Janar ‘yansandan Nijeriya ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan kisan ‘yansandan da aka samu a baya-bayan nan.