Cikin kusan shekaru 10 da suka gabata, mahukuntan jihar Tibet mai cin gashin kanta dake kudu maso yammacin kasar Sin, sun kashe kudaden da yawansu ya kai yuan biliyan 12.7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.8 a fannin kare muhallin halittu.
Da take bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a jiya Litinin, mataimakiyar shugaban sashen lura da muhallin halittun da sauran muhallin zaman al’umma Shui Yanping ta ce, a shekarar 2021, adadin fadin dazukan Tibet ya kai kaso 12.31 bisa dari na daukacin fadin jihar, yayin da sassan dake lullube da tsirrai ya karu zuwa kaso 47.14 bisa dari.
A daga bangaren kuma, adadin dabbobi dake daf da karewa, wadanda aka yi nasarar farfado da yawansu shi ma ya yi matukar karuwa.
Adadin shamuwa mai bakin wuya ya karu daga kasa da 3,000 a shekarar 1995, zuwa sama da 10,000 a yanzu, wadda ta kasance daya daga na sahun gaba, cikin dabbobin da ake karewa a Sin, yayin da yawan Barewar Tibet shi ma ya karu zuwa sama da 300,000.
Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, jihar Tibet na cikin yankunan duniya mafiya kyawun yanayi, saboda yadda muhallin halittun jihar ke cikin yanayi na daidaito, kuma muhallin rayuwar al’umma ke kara kyautata. (Saminu Alhassan)