A gun zama na 18 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, an jefa kuri’u a yau Jumma’a 24 ga wannan wata tare da zartas da kudurin kebe ranar 25 ga watan Oktoba a matsayin ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, don haka an sanya ranar bisa dokoki da kuma gudanar da bukukuwa ta hanyoyi daban daban don tunawa da ranar.
Kudurin ya yi nuni da cewa, kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan, muhimmiyar nasara ce da kasar Sin ta samu yayin yakin yaki da maharan Japan, kana muhimmiyar alama ce da gwamnatin kasar Sin ta mayar da ikon mallakar kasa a yankin Taiwan, da kuma shaida cewa, yankin Taiwan yanki ne na kasar Sin bisa tarihi da dokoki, kana ranar ta zama rana mai alfahari ga jama’ar gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan da ma dukkan jama’ar kasar Sin baki daya.
Darektan kwamitin kula da ayyukan tsarin dokoki na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Shen Chunyao ya yi bayani game da kudurin cewa, a ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 1945, an gudanar da bikin mika ikon mallakar yankin Taiwan ga kasar Sin, tun daga wannan lokaci, an dawo da ikon mallakar yankin Taiwan da tsibiran Penghu ga kasar Sin. Kafa ranar tunawa da kawo karshen mulkin mallakar Japan a yankin Taiwan da dawo ikon mallakar yankin a kasar Sin, ya shaida cewa yankin Taiwan yanki ne na kasar Sin a tarihi, da jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su tsaya tsayin daka kan ka’idar Sin daya tak a duniya, da kuma sa kaimi ga jama’ar kasar Sin wajen yin kokarin samun dinkuwar dukkan yankunan kasa da farfado da al’ummar kasar da kuma hadin kan kasar baki daya. (Zainab Zhang)













