Tun daga yau Asabar 5 ga wata, aka kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin daga ketare wato CIIE karo na biyar a birnin Shanghai, inda aka kebe rumfunan nune-nune guda shida wadanda suka hada da rumfar abinci da amfanin gona, da motoci, da na’urorin fasaha, da ta kayayyakin masarufi, da kayayyakin kiwon lafiya da kuma rumfar hidimar cinikayya.
Ban da haka, wannan shi ne karo na farko da aka kafa hadaddiyar rumfar nune-nune mai taken “Kasar Sin a shekaru goma da suka gabata wato sakamakon da kasar Sin ta samu wajen bude kofa ga ketare”.
Rumfar nuna abinci da amfanin gona, rumfa ce da ta fi samun karbuwa, inda ta samu halartar kamfanoni mafiya yawa, inda adadin kamfanonin da suka zo daga kasashe da yankuna sama da 100 ya zarce 1000.
Abun farin ciki shi ne, a karo na farko an kafa wani wurin musamman domin nuna nau’o’in hatsi, inda za a shirya dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin manyan kamfanonin kasa da kasa da kungiyar kula da ire-iren hatsi ta kasar Sin.
Kana an baje sabbin sakamakon da aka samu a bangaren masana’antun kera motoci a rumfar nuna motoci, bisa taken “Amfani da fasahohin zamani” da kuma “Rage fitar da iskar dake gurbata muhalli ”. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)