A wani gagarumun taron daurin aure na Nabila Kabir da ya hada mataimakan shugabanin jami’o’i da cibiyoyin ilimin Nijeriya daban-daban da dinbin farfesoshi da sauran al’uma sun yi jawabi awurin wanda ya gudana a jami’ar Bayero ta Kano a ranar Asabar da ta gabata.
Masana da sauran mahalarta taron sun yi tsokaci a kan yadda ya kamata aure ya kasance musamam auren Hausawa mai dogon tarihi, tasiri, albarka da dai sauransu.
- Manoman Alkama 200 Za Su Amfana Da Shirin NALDA A Jihar Jigawa
- Kasar Sin Za Ta Kafa Karin Yankunan Misali 29 Na Inganta Shigo Da Kayayyaki Kasar
Farfesa Sani Malumfashi, masani ne a kan halayya da zamantakewar Dan’adam ya ce abun sha’awa a auren Hausawa shi ne, yadda malam Bahaushe yake da kaunar domin a kan iya daukar kudin sallamar aiki ko fansho ko a saida gona ko gida da sauransu saboda a yi aure, wannan ya nuna babu wanda ya fi Bahaushe san aure da ba shi muhimanci.
Ya ce wani abu da ke bukatar gyara a auran Hausawa shi ne, a kan samu wasu daga cikin wadanda za su yi auren ko suka yi ba su shirya wa zaman auran ba, ta fuskar ilimin auren da daukar nauyinsa, wanda hakan ce take sa a samu wasu na neman taimako kan za su biya sadaki ko za su sayi ragon suna, da sauran bukatu wanda shari’a ba ta daura musu dole ba.
Shi kuwa, Farfesa Kabir Bello Dumbulun, wanda shi ma masanin halayar Dan’adam ne da zamantakewa na jami’ar Bayero cewa ya yi akwai bukatar sanin cewa aure fa ibada ne, kuma ibada aiki ne na neman lada a wurin Allah.
Malan Usman Sarki wanda aka fi sani da SK masani a kan kididigar yawan jama’a, ya ce duk abun alkairi sai an hada da hakuri, domin cimma burin duniya da lahira.