Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da cikakken atisayen hadin gwiwa na karshe a yau Talata ga kumbon Shenzhou-20 na kasar Sin.
Daukacin na’urori da manhajojin aiki da ake son amfani da su a binciken sun yi nasarar tsallaka gwaje-gwajen aiki, inda kayan aikin da aka tanadar suka yi aiki ba tare da tangarda ba, kana ‘yan sama jannatin kumbon su ma sun shirya tsaf.
- Illolin Da Manufar Haraji Kan Kayayyaki Ta Haifar A Kan Amerikawa
- Shettima Ya Gayyaci Shugaban NAHCON Da Mambobin Hukumar Kan Shirye-shiryen Hajjin 2025
A halin yanzu, masana kimiyyar yanayi suna sa ido sosai kan yanayi domin lura da yadda lokacin da ake son harba kumbon zai kasance.
Har ila yau, an rubanya ayyukan tuntubar da ake yi game da yanayi da kuma gudanar da bincike na musamman kan yiwuwar wargajewar da za a iya samu daga yanayin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp