A lokacin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ke gab da ziyartar kasar Faransa cikin kwanaki masu zuwa, kungiyar hulda da kasashen waje ta jama’ar kasar Sin, da babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG, da ofishin jakadancin Sin dake kasar Faransa, sun kira taron dandalin tattaunawa kan musayar al’adu tsakanin bangarorin Sin da Faransa, jiya Talata a birnin Paris na kasar Faransa.
Da ya ke jawabi ga taron ta kafar bidiyo, shugaban CMG Shen Haixiong ya ce, kasashen Sin da Faransa suna da al’adu masu daraja, wadanda suka taka muhimmiyar rawa a tarihin dan Adam.
Ya ce a nashi bangare, CMG na kokarin watsa bayanai da shirye-shirye, masu alaka da zumuntar dake tsakanin bangarorin Sin da Faransa, da zummar karfafa cudanya tsakanin al’ummun kasashen 2, da sa kaimi ga musaya da koyi da juna ta fuskar al’adu.
Mista Shen ya kara da cewa, CMG na son yin kokari tare da abokai masu sana’o’i daban daban na kasar Faransa, don samar da gudunmowa a yunkurin tabbatar da makoma mai haske ta huldar dake tsakanin kasashen 2. (Bello Wang)