An kori wata jarumar fim Melissa Barrera daga fitowar gaba ta wani fim mai dogon zango Scream bayan masu shirya fim din, sun ce sakonnin da take wallafawa don goyon bayan Falasdinawa a shafukan sada zumunta, na kin jinin Yahudawa ne.
Tauraruwar a kai a kai tana wallafa sakonni game da rikicin Isra’ila da Gaza, ciki har da wani sako da ta sake yadawa wanda ke zargin Isra’ila da aikata “Kisan kare dangi da shafe wata al’umma daga doron duniya”.
- Gwamna Uba Sani Ya Kafa Kwamitin Binciken Matsalolin Aiki Hajji
- Kamfanonin Nijeriya Sun Kara Wa Ma’aikatansu Albashin Naira Tiriliyan 4.6 Cikin Wata 6 -NBS
Kamfanin shirya fina-finai na Spyglass ya ce yana da manufar “rashin lamuntar kin jinin Yahudawa daidai da kwayar zarra”.
A lokaci guda, ita ma Susan Sarandon an watsar da ita daga harkokin shirya fim bayan ta gabatar da jawabi a wani taron nuna goyon bayan Falasdinawa.
Daga Susan Sarandon, wadda ta bayyana a fim din Thelma & Louise, har zuwa kan jaruma Melissa Barrera ‘yar Medico, babu wadda ta mayar da martani kan lamarin.
Sai dai, kafin ba da sanarwar fitar da ita, Melissa Barrera ta sake yada wani sako a shafinta na Instagram da ke cewa: “A karshe dai, na gwammace a cire ni saboda wanda na shigo da shi cikin harkokina a kan a shigar da ni saboda wanda na cire.”
Wasu masu bibiyar tauraruwar sun yi wa sakon fashin bakin cewa hakan yana nuni ne da batun korar ta daga fim din.
Barrera ta jagoranci fina-finan Scream guda biyu a baya kuma ta bayyana a matsayin tauraruwa a wani fim mai suna Carmen da kuma wani baddalallen fim mai suna The Heights.
Sauran sakonnin da tauraruwa Barrera ta sake yadawa a makonnin baya-bayan nan akwai wani kan yadda aka jirkita batun kisan kare dangin da aka yi wa Yahudawa na Holocaust “don bunkasa masana’antun kera makaman Isra’ila” da kuma wannan da ke cewa Gaza “a yanzu ta koma kamar wani sansanin azabtarwa ne”.