Kakakin rundunar tsaron teku ta kasar Sin Liu Dejun, ya bayyana a yau Lahadi cewa, an kori wani jirgin kamun kifi na kasar Japan da ya shiga yankin ruwan kasar Sin na tsibirin Diaoyu Dao ba bisa ka’ida ba.
A cewarsa, rundunar ta dauki matakan da suka dace bisa doka, ta gargadi jirgin sannan ta kore shi, bayan ya shiga yankin ruwan kasar Sin tsakanin ranar Asabar da Lahadi.
- Sau Biyu Ake Yin Girbin Aya A Shekara – RMRDC
- Gwamnatin Yobe Ta Ƙaryata Rahoton Bayyanar Boko Haram A Babban Birnin Jihar
Da yake bayyana tsibirin na Diaoyu Dao da tsibiran dake karkashinsa a matsayin mallakin kasar Sin, Liu Dejun ya bukaci Japan ta gaggauta dakatar da ayyukanta da suka saba doka a wadannan yankuna.
Har ila yau, rundunar ta ce, za ta ci gaba da ayyukanta na tabbatar da doka a yankin ruwa na tsibirin Diaoyu Dao da kare yankuna da hakkoki da muradun kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp