Wata kotun hukunta manyan laifuka ta Jihar Legas da ke Ikeja ta gurfanar da wani tsohon manajan banki reshen Iju, Abiodun Sanni, a gidan yari bisa zargin damfarar Naira miliyan 122,011,441.
Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, ta gurfanar da Sanni a gaban kuliya 16 da suka hada da karbar bashi ta hanyar karya, amfani da takardun karya da kuma sata.
- Bankin Duniya Da IMF Na Kassara Tsarin Ilimin Jami’o’i A Nijeriya – ASUU
- Karancin Kudin Shiga Ya Jefa ‘Yan Nijeriya Miliyan 14 Cikin Kangin Talauci – Bankin Duniya
Lauyan masu shigar da kara na EFCC, O. Adewunmi, ya shaida wa kotun cewa Sanni ya aikata laifin ne a ranar 24 ga Fabrairu, 2020, a Legas.
Adewunmi ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara a lokacin yana manajan bankin Polaris Bank Limited reshen lju, ya samu rance ne a matsayin rancen kudi Naira miliyan 17, kan wani Bamgbose Tayo Taofia da ke kasuwanci da suna da salon Banut Haulage. .
Mai gabatar da kara ya bayyana cewa, an samu kudin ne daga bankin Polaris Bank Limited, ta hanyar karyar cewa bashin na da garantin ne a wani kayyade a asusun ajiya mai lamba 0071572791, kudin da ya kai Naira miliyan 111,540,380.52 mallakin Yinkus Multibiz Bentures da kuma mai ita, daya Misis Olayinka. Hannah Aderibigbe, ta amince a yi amfani da shi a matsayin jingina.
Haka kuma an zarge shi da rashin gaskiya da canza wani asusun ajiya na Polaris Bank Limited mai lamba 0071277522 akan kudi Naira miliyan 15, 011,441.00 (Miliyan Goma Sha Biyar, Dubu Sha daya, Dari Hudu da Arba’in da Daya) mallakar Atolagbe Joshua Tinuoye, zuwa amfani da shi.
Sai dai wanda ake tuhumar ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Lauyan mai gabatar da kara, ya bukaci kotun da ta ci gaba da tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali, har zuwa lokacin da za a fara shari’a.
“Ya Ubangiji, mai gabatar da kara ya yi niyyar gabatar da shaidu 10 game da wannan shari’a kuma muna rokon kotu ta tsare wanda ake kara a gidan yari”, in ji Adewunmi.
Sai dai lauyan da ake kara, Osho Oludoshu, ya shaida wa kotun cewa ya shigar da bukatar neman beli a madadin wanda yake karewa.
A wani takaitaccen hukunci mai shari’a Olubunmi Abike-Fadipe, ta dage ci gaba da sauraron karar tare da bayar da umarnin mika bukatar belin ga kotu kafin ranar da za a fara shari’ar.
“Na dage shari’ar zuwa Match 6 da 19, 2025, kuma na tsare wanda ake kara a gidan gyaran hali. Suna da damar gabatar da takardar neman beli kafin ranar shari’arsa,” in ji alkalin.