Za a iya cewa idan za a yi la’akari da abubuwan da suka faru a wasan karshe da Paris St-Germain ta buga, akwai alamun cewa za a samu abubuwan ban mamaki a ‘yan watannin da suka rage wa Kylian Mbappe a kungiyar.
Mbappe ya amince ya koma Real Madrid a wannan bazarar, kuma duk da cewa PSG ba ta tabbatar da hakan a hukumance ba alamu sun fara nuna cewa ta fara shirin rayuwa ba tare da dan wasan ba.
- Kafa Jam’iyyar Adawa: Atiku Da Wasu Sanatoci Sun Sake Sabon Yunkuri
- Ana Amfani Da Na’urar Hakar Mai Ta Zamani Da Kamfanin Sin Ya Kera A Uganda
A karawar da ta yi da Monaco a ranar Juma’ar da ta gabata, inda wasan ya kare babu ci, an cire Mbappe ne a lokacin hutun rabin lokaci amma maimakon zama tare da takwarorinsa a bencin PSG, Mbappe ya zabi ya zauna tare da mahaifiyarsa a cikin ‘yan kallo.
Yanzu dai an sauya Mbappe a wasanni biyu a jere, inda aka maye gurbinsa bayan mintuna 65 a wasan da suka tashi 1-1 da Rennes bayan ya kasa zura kwallo a raga a wasan.
Sai dai kociyan kungiyar ta Paris Saint German, Luis Enrikue, ya bayyana cewa ko ba-jima ko ba-dade sai sun fara sabawa da wasa ba tare da dan wasa Kylian Mbappe ba a kungiyar.
Dan wasa Mbappe ya ci wa PSG kwallaye 26 a dukkan gasa a kakar wasa ta bana, inda 21 daga cikinsu suka zo a gasar Ligue 1 wanda ya sa ya zama kan gaba a jerin masu cin kwallo a gasar.
PSG dai tana kan hanyar kare kambunta na gasar kasar Faransa inda take da tazarar maki tara tsakaninta da Brest wadda ke a matsayi na biyu amma kuma yayin da nasarorin cikin gida suka zo cikin sauki ga PSG a karkashin mallakar ‘yan Katar, samun nasara a gasar zakarun Turai ya faskara.
Idan aka yi la’akari da tarihin bajintarsa a gasar, da alama PSG za ta yi wa kanta sakiyar da babu ruwa idan har ba ta samu abin da ya kamata ba daga shararren dan wasan na duniya kafin ya tafi.
Sai dai shima Mbappe ya ce ba shi da matsala da kociyan kungiyar ta PSG Luis Enrikue, ya bayyana haka ne a ranar da ya zura kwallaye biyu a gasar cin kofin zakarun Turai da suka doke Real Sociedad wanda hakan ya sanya PSG ta ketara zuwa zagayen dab da na kusa da na karshe.
Tun bayan da ya bayyana aniyarsa ta barin Parc des Princes, masu bibiyar harkar kwallon kafa sun sanya alamar tambaya kan zamantakewarsa da Enrikue, inda ake ajiye dan wasan a benci ko kuma an cire shi da wuri, musamman wasannin PSG uku na baya-bayan nan a gasar Ligue 1.
Amma Mbappe ya ce ” A koyaushe ina son buga gasar Zakarun Turai, gasa ce mai matukar muhimmanci. Ba zan taba zama dan wasan dake buya ba sannan dangantaka ta da kocina na da kyau, babu matsala ko da mutane za su yi tunanin cewa akwai. Ina da matsaloli da yawa amma kocin ba ya cikinsu.”