Gwamnatin Nijeriya ta sake kwashe ‘Yan ƙasar 126 daga Sudan sakamakon rikicin da ake yi a ƙasar tsakanin sojoji da rundunar RSF.
BBC ta rawaito cewa, Mutanen da jirgin kamfanin Tarco ya ɗebo sun sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 4:56 na yammacin jiya Asabar.
- ‘Yan Nijeriya 125 Da Suka Makale A Sudan Za Su Iso Abuja Yau Asabar
- Tarihin Tsohon Shugaban Kasar Sudan Omar el-Bashir
Hukumar agajin gaggawa ta Nijeriya, NEMA, ita ce ta jagoranci ɗebo mutanen tare da haɗin gwiwar ma’aikatun harkokin waje da ta ‘yan Nijeriya mazauna ƙetare, da sauransu.
Talla
Sai dai har yanzu akwai ɗaruruwan ‘yan Najeriyar da ke roƙon a kwashe su daga Sudan ɗin amma babu tabbas ko gwamnatin ƙasar za ta ci gaba da aikin kwashe su a yanzu.
Talla