An gurfanar da wani mutum mai suna Okwudili Orji mai shekaru 42 a gaban kotu bisa zargin satar sandunan karafa da kudinsu ya kai Naira miliyan 5 a yankin Ejigbo da ke Jihar Legas.
An gurfanar da Orji ne a kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi sata a gaban babban alkalin kotun majistare Patrick Nwaka a kotun Majistare ta Yaba.
- Sin Ta Bukaci Japan Da Kada Ta Yi Yunkurin Amfani Da Rahoton IAEA A Matsayin Izinin Zubar Da Dagwalon Ruwan Nukiliya A Cikin Teku
- Ina Son Kara Aure, Ko Me Yake Kawo Matsaloli Tsakanin Kishiyoyi Da Yadda Za A Magance?
Dan sanda mai shigar da kara, Cyril Ejiofor, ya shaida wa kotun cewa laifukan da Orji ya aikata sun saba wa sashe na 314 da 287 na dokar laifuka ta Jihar Legas a shekarar 2015.
A wani bangare na tuhume-tuhumen, ya kara da cewa, “Kai Okwudili Orji, a cikin watan Satumba 2022, da misalin karfe 9 na safe, a mahadar Bucknor, Ejigbo, Jihar Legas, a gundumar Majistare ta Legas, ka yi damfara da sandunan karfe da kudinsu ya kai Naira miliyan 5, daga wani mutum Uzoma Patrick, da ya zama shi ne wakilinku, bayan ka san damfara ce, don haka laifin da ka aikata zai kai ga hukunka shi a karkashin sashe na 314 na dokar laifuka ta Jihar Legas na shekarar 2015.”
Lauyan da yake kare wanda ake kara, N.C. Okparauwa, ya roki kotun da ta amince da wanda yake karewa a ba da belinsa a mafi saukin yanayi domin ya samu sukunin kara bincke.
A cewarsa bai ga wata hujja a kan karar da masu gabatar da kara suka gabatar ba, alkalin kotun ya amince wanda ake kara ya bayar da belinsa a kan kudi Naira 1 tare da mutum biyu da za su tsaya masa.
Ya ba da umarnin cewa wadanda za su tsaya masa dole su zama ma’aikata ne masu daraja a Jihar Legas ba masu sana’o’in dogaro da kai ba, sannan kuma dole ne su gabatar da takardar shaidar biyan haraji na shekaru uku da kotu za ta iya tantancewa.
Mai shari’a Nwaka ya dage sauraron karar har zuwa ranar 28 ga Agusta, 2023, domin ci gaba sauraro.