Babbar kotun Jihar Bauchi mai lamba 6 ta yankewa Yusuf Bako mai shekaru 50 hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bisa samunsa da laifin yi wa wata yarinya fyade a cikin wani masallaci.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa an kama Bako ne a shekarar 2020 da aikata laifin, inda ya amsa laifinsa.
- Ganduje Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Na’Abba
- Da Sannu Za Mu Farfado Da Manchester United – Jim Ractliffe
An zarge shi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara hudu fyade a cikin masallaci yayin da ake tsaka da kulln COVID-19.
Wannan ba shi ne laifinsa na farko ba, a baya an daure shi sau biyu a kan laifukan fyade a jihar.
Darakta mai shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta Jihar Bauchi, Barista Sha’awanatu Yusuf, ta tabbatar da hukuncin a wata tattaunawa ta musamman da ta yi da wakilinmu a ranar Laraba.
Ta ce mai shari’a Sa’ad Zadawa na babbar kotu mai lamba 6 ne, ya yanke hukuncin a karshen watan Nuwamban bana bayan sauraron karar da bangarorin biyu suka yi.
Sha’awanatu ta bayyana cewa, wannan hukunci na nuni da kudirin ma’aikatar wajen tabbatar da adalci ga wadda aka yi wa fyade da kuma tabbatar da ingancin dokar VAPP da ke aiki a jihar.
Ta yi kira ga iyaye da su hada kai da hukumomi wajen gurfanar da duk wanda ake zargi da aikata laifin fyade.
“Wasu iyaye suna hana ‘ya’yansu da aka yi wa fyaden su gurfana a gaban kotu su ba da shaida,” in ji Sha’awanatu.
Wani abin lura a nan shi ne, a shekarar 2022, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya amince da dokar VAPP, wadda ta tanadi hukuncin kisa da daurin rai da rai ga wanda aka samu da laifin aikata fyade.